An yi garkuwa da awakin wani dan siyasa

Asalin hoton, Getty Images
An sace awakin wani dan siyasa da ke kudancin Habasha "a wani yunkurin hana shi yin siyasa," a cewar shugaban jam'iyyar adawa ta Arena Tigray kamar yadda ya shaida wa BBC.
Awakin guda 16 an sace su ne daga wata gona da ke kusa da Zenawi Asmelash kusa da wani wurin jami'an tsaro a Kola Temben, yankin Tigray a ranar Laraba, a cewar Abrha Desta.
Shugabannin jam'iyya mai mulki ta TPLF sun kama Mista Zenawi a baya kuma sun yi masa barazana, a yanzu sun biyo ta hanyar awakin nasa a matsayin wata hanya in ji shugaban jam'iyyar adawa.
Arena Tigray kafaffiyar jam'iyyar adawa ce wadda ke ci kuma take kokarin kara yawan mambobinta a shirin zaben da za a yi a shekara mai zuwa.
Labarin ya jawo ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta a Habasha bayan Mista Abrha ya bayyana a shafin Facebook cewa "TPLF sun zama dabbobi ba mutane ba"
Wasu sun mayar da kalaman abin wasa, wasu kuma sun nuna damuwa a kan kalaman inda wasu suka fara gangamin "a saki awakin da aka kama domin siyasa."
Wasu kuma sun dauki lamarin da muhimmanci suna ganin cewa cin zali ne na siyasa.
Shugaban 'yan sandan yankin ya tabbatar wa da BBC cewa an sace awakin, amma ba zai ba da cikakken bayani kan lamarin ba.
Uku daga cikin awakin sun fita daga inda aka tsare su inda suka koma gida, amma har yanzu 13 na a tsare a cewar Mista Zenawi.
Jam'iyyar TPLF ba ta yi maganta a kan lamarin ba i zuwa yanzu.











