Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An yi garkuwa da 'yan mata Turawa a Ghana
Wata kafar watsa labaran Canada ta tabbatar da rahotannin da ke cewa, an sace wasu `yan mata 'yan kasar ta Canada su biyu a Ghana, da daren Laraba.
Rahotanni na cewa an sace `yan kasar ta Canda ne a birnin Kumasi da ke jihar Ashanti.
Wasu rahotanni na cewar jami`an tsaro a jihar ta Ashanti sun baza komarsu don neman mutanen biyu da wani gungun mutane ya yi garkuwar da su.
An dai ce da misalin karfe takwas na daren Laraba ne wasu mutane dauke da bindiga su ka sace 'yan matan a wani shaharrrin wurin shakatawa da ke birnin na Kumasi.
Rahotanni sun bayyana sunan daya daga cikin wadanda aka sace da Lauren da abokiyar tafiyarta wadda suka zo wani shirin musayar ilimi a jami`ar Kumasi Technical Univeristy
Tuni ofishin jakandancin kasar ta Canada a Ghana ya shiga aiki tare da `yan sanda don ceto mutanen.
Wannan shi ne karo na biyu da ake sace dan wata kasa a birnin na Kumasi, inda a kwanakin baya aka sace wani dan kasar Indiya kafin daga bisani `yan sanda su kubutar da shi.