Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Matan Ghana sun fi na Najeriya ina soyayya da aminci
Latsa hoton sama domin ka kalli bidiyon
Wani dan Najeriya wanda ya kwashe shekara takwas a kasar Ghana, Mosses Balogun wanda kuma yake auren wata 'yar Ghana ya bayyana cewa iya soyayya ya sa ya auri 'yar Ghana a maimakon 'yar Najeriya.
A cewar Mosses, matan Ghana sun fi 'yan matan Najeriya iya soyayya da kuma aminci.
Balogun ya ce, ya taba yin soyayya da wata 'yar Najeriya amma ba su kwashe da dadi ba saboda yaudarar sa da ta yi daga karshe.