Ana zanga-zangar cire tallafi a kan biredi da man fetur a Sudan

Shugaba Omar Al-Bashir

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Shugaba Omar Al-Bashir

Masu zanga-zanga a Sudan sun nuna rashin jin dadinsu kan shirin da gwamnati ke yi na cire tallafi a kan biredi da man fetur.

Wani bidiyo da aka wallafa a shafin twitter ya nuna yanda dandazon mutane suka fito a titunan arewacin Atbara da Port Sudan inda shugaban kasar Omar Al-Bashir yake ziyarta.

Rahotanni sun bayyana cewa ana samun matsala ta fannin sadarwa a kasar wanda hakan ya ja ake shan wahala wurin amfani da wayoyin salula.

Firayim ministan Sudan Motazz Moussa yayi bayani a wurin wani taron manema labarai a ranar laraba, inda ya bayyana cewa ba za'a cire tallafin gaba daya ba.

''Ba za a cire tallafi ba, kuma za a kawo sabbin tsare-tsare da zasu bada tallafi ga wadanda suke bukata, saboda bazamu iya kara wa mai karfi karfi ba.'' in ji shi.

Ministan ya kara da cewa gwamnati tana bayar da tallafin man fetur da kusan kashi 90 cikin 100.

Yanzu haka dai an sa dokar hana fita kuma an dauke wutar lantarki a Atbara.

Sudan dai ta kwana biyu tana fama da matsin tattalin arziki tun bayan da Sudan ta kudu ta fita daga kasar inda ta samu mafi tsokar arzikin man fetur.