Kalli hotunan zanga-zangar 'yan Sudan a Ghana

Wasu 'yan gudun hijirar Sudan a Ghana sun yi zanga-zangar lumana a gaban ofishin majalisar Dinkin Duniya da ke Accra, babban birnin kasar inda suka bukaci a samar masu da abubuwan more rayuwa sannan a ba su mafaka.

Ghana
Bayanan hoto, Maza da mata da yara sun fito kwansu da kwarkwatarsu don nuna rashin jin dadinsu kan irin rayuwar da suke yi a Ghana.
Ghana
Bayanan hoto, Masu zanga-zangar dai na bukatar a sama masu abubuwan more rayuwa kamar muhallai da kiwon lafiya.
Ghana
Bayanan hoto, Cikin masu zanga-zangar har da mata da yara rike da kwalaye da ke dauke da kalaman neman agajin abinci da muhalli.
Ghana
Bayanan hoto, Masu zanga-zangar sun yi jerin gwano a bakin titi rike da kwalaye a gaban ofishin Majalisar Dinkin Duniya.
Ghana
Bayanan hoto, Cikin masu zanga-zangar har da mata da yara rike da kwalaye da ke dauke da kalaman neman agajin abinci da muhalli.
Ghana
Bayanan hoto, Da yawa daga cikin mutanen dai 'yan gudun hijira ne daga yankin Darfur da yaki ya daidaita.
Ghana
Bayanan hoto, Sun rike kwalaye masu dauke da rubutun da ke bayyana bukatunsu na samun damar yin rayuwa kamar sauran jama'ar kasar.
Ghana
Bayanan hoto, Da yawa daga cikin mutanen dai 'yan gudun hijira ne daga yankin dargur da yaki ya daidaita.