Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kalli hotunan zanga-zangar 'yan Sudan a Ghana
Wasu 'yan gudun hijirar Sudan a Ghana sun yi zanga-zangar lumana a gaban ofishin majalisar Dinkin Duniya da ke Accra, babban birnin kasar inda suka bukaci a samar masu da abubuwan more rayuwa sannan a ba su mafaka.