Red Cross: Wa'adin da Boko Haram ta bayar ya kusa cika

Kungiyar bayar da agaji ta The International Committee of the Red Cross (ICRC) ta yi kira na gaggawa ga gwamnatin Najeriya da ta taimaka wurin sakin ma'aikatanta biyu da ke hannun mayakan Boko Haram.

Wata sanarwa da mai magana da yawun kungiyar a Najeriya Aleksandra Matijevic Mosiman ta aikewa manema labarai ranar Lahadi ta yi kira da 'yan Boko Haram su saki Hauwa Mohammed Liman da Alice Loksha, ma'aikatan jinya da suka sace a farkon shekarar nan.

Red Cross ta ce wannan kiran na gaggawa ya zama wajibi saboda labarin da ta samu cewa nan da sao'i 24 mayakan Boko Haram za su kashe daya daga cikin ma'aikatan nata.

A watan Maris mayakan Boko Haram suka sace ma'aikatan na Red Cross uku wadanda ke aikin ba da agaji a garin Rann na jihar Borno.

A watan jiya kuma suka kashe daya daga cikin su mai suna Saifura Hussaini Ahmed Khorsa, lamarin da ya jawo allawadai daga dukkan bangarorin al'umma.

"Muna kira ga mutanen da suka sace wadannan mata, ISWAP (Islamic State's West African province group) da su nuna jinkai. Don Allah kada ku kashe su domin ma'aikatan lafiya ne da basu ji ba basu gani ba, wadanda ke taimaka wa al'umomin arewa maso gabaahin Najeriya," sanarwar ta ambato babban jami'in ba da agaji na kungiyar a yankin Lake Chad, Mamadou Sow, yana cewa.