An kama masu garkuwa da gawa a Imo

'Yan sanda sun kama wasu mutane biyu da ake zargi da garkuwa da gawar wata tsohuwa a jihar Imo da ke kudu maso-gabashin Najeriya.

'Yan sandan sun ce mutanen sun sace gawar ne daga wajen ajiye gawa a wani asibiti, kuma suka kai ta daji suna neman naira miliyan hudu a matsayin kudin fansa daga asibitin da kuma iyalan marigayiyar.

Bayan wani binciken kwakwaf na bin diddigi ne 'yan sandan suka ce sun yi nasarar kama wadanda ake zargin, wadanda daman a kwanan nan aka sako su daga kurkuku bayan hukuncin satar mutane, suka kuma kai 'yan sanda daji inda suka boye gawar, aka dauko ta.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar ta Imo DSP Enwerem Andrew ya ce wannan salon sata ne da su taba ganin irin ta ba.

A Najeriya dai ansaba yin garkuwa da mutane dan neman kudin fansa daga 'yan uwan wadanda aka sace.

Amma garkuwa da gawa lamari ne da a iya cewa shi ne irinsa na farko a dan tsakanin, da gwamnati ta sha damarar magnce satar mutane a kasar.