Zamfara: 'Yan fashin shanu sun koma satar mutane

Asalin hoton, Getty Images
A Najeriya, yayin da bisa ga dukkan alamu shanun da ake yawan sacewa a wasu sassa na jihar Zamfara suka kare, a yanzu masu tafka wannan al'amari sun bullo da wata sabuwar ta'asa.
Inda suke bi suna sace mutanen kauyuka, sai an biya kudin fansa su sako wadanda suka sace.
A zancen da ake yanzu haka, akwai mutane fiye da goma da aka sace a maraicen jiya a garin Bindin na yankin karamar hukumar Maru a jihar ta Zamfara.
Sai dai rundunar 'yan sandan jihar ta ki ta ce uffan game da wannan batu kamar yadda zaku ji a Rahoton AbdusSalam Ibrahim Ahmed.







