Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wa ya fi cin wani tsakanin Real Madrid da Bayern Munich?
Bayern Munich da Real Madrid sun fafata a wasan dab da na karshe a gasar cin kofin zakarun Turai, inda Real ta yi nasara da ci 2-1.
An yi karawar farko ne a filin wasa na Allianz Arena da ke Munich, kuma duka kungiyoyin biyu na fatan kaiwa gaci.
Wannan ne karo na 26 da suka kara da juna a gasar Turai - kuma ita ce haduwa mafi yawa da aka taba yi tsakanin wasu kungiyoyi biyu.
Real Madrid da samu nasara sau 12 yayin da Bayern ta ci karawa 11 a tarihin haduwarsu.
Wannan shi ne karo na uku tun shekarar 2011-12 da Bayern da Real suka hadu da juna a wasan dab da na karshe.
Bayern ta samu nasara a 2011-12 yayin da Madrid ta kai gaci a 2013-14.
Bayern ta sha kashi a wasanninta biyar na baya-bayan nan da ta fafata da Madrid a gasar zakarun Turai.
Kocin bayern Jupp Heynckes ya samu nasara a wasa 14 cikin 16 da ya buga a filin wasa na Allianz Arena a gasar zakarun Turai (canjaras daya, rashin nasara daya), inda Bayern ta zura kwallo 48 sannan aka ci ta 10.
Cristiano Ronaldo ya zura akalla kwallo daya a duk wasa 11 na baya-bayan nan da ya buga a gasar (kwallo 17 jumulla).
Wannan ita ce bajinta mafi kyau da wani dan wasa ya taba yi a tarihi.
Dan wasan mai shekara 33 ya ci kwallo tara a ragar Bayern Munich a gasar zakarun Turai.
Shi ne dai dan wasa daya tilo da ya ci kwallo fiye da haka a ragar wata kungiya, inda ya zura kwallo 10 a ragar Juventus.
Wannan wasa zai kuma hada 'yan wasan da suka fi kowa zura kwallo a wasan dab da na karshe na gasar- Cristiano Ronaldo ya zura 13 a wannan mataki, yayin da Robert Lewandowski ya ci shida.