Mutum 36 sun mutu a hatsarin mota a Kenya

Asalin hoton, AFP/Getty
Fiye da mutum 36 suka mutu a wani mummunan hatsarin mota tsakanin wata motar fasinja da mai dakon man fetur.
Hatsarin ya auku ne da safiyar Lahadi a garin Salgaa dake kimanin kilomita 200 yamma da birnin Nairobi, inda fiye da mutum 12 suka jikkata.
A sanadiyyar wannan hatsarin, hukumar sufurin da kiyaye hatsurra ta Kenya ta dakatar da tafiye-tafiyen dare ga motocin sufuri masu dogon zango.
"Ina barci a lokacin da hatsarin ya auku, kawai naji wani kara ne da ihun mutane kafin aka taimaka aka fitar da ni." Wani fasinja kenan wanda ya tsira da ransa a wata hira da wata tashar rediyo dake yankin.
Rahotanni sun ce duka direbobin motocin sun rasa rayukansu, kuma akwai wani yaro dan shekara uku a cikin fasinjojin da suka mutu.
Hukumar kuma ta bayyana cewa hatsarin, wanda ya auku da misalin karfe 3 na dare, ya auku ne a sanadiyyar wani taho mu gama tsakanin wata motar fasinja mai daukar mutum 62 da wata tankar man fetur a wani wuri da yayi kaurin suna sabili da yawan hatsura.
Kungiyar Red Cross ta Kenya ta tabbatar da mutuwar mutum 36.

Asalin hoton, AFP/Getty
Sauran wadanda suka sami raunuka an kai su babban asibitin garin Nakuru da wasu asibitocin dake garuruwan dake kusa.
A farkon watan Disamba, fiye da mutum fiye da 20 ne suka halaka a wani hatsarin mota a daidai wannan wurin.
Kuma hukumar sufuri da kiyaye hatsurra ta kasar ta ce ta damu da yadda ake asarar rayuka kimanin 3,000 a kowace shekara, ta a dalilin hatsurran mota a fadin kasar.
A bana kadai, mutum 2,883 ne suka halaka a a kan wannan hanyar, kuma mutum 300 a cikinsu sun mutu ne a watan nan na Disamba.
Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce Kenya na gaba-gaba a kasashen duniya da aka fi samun aukuwar hatsurra.











