PSG ta kammala daukar Neymar

Asalin hoton, Getty Images
Paris St-Germain ta kammala daukar Neymar daga Barcelona kan kudi fam miliyan 200 a matsayin dan kwallo mafi tsada a tarihi a duniya.
Cinikin dan wasan na tawagar Brazil mai shekara 25, ya haura wanda Manchester United ta sayi Paul Pogba daga Juventus a Agustan 2016 kan fam miliyan 89.
Neymar zai karbi albashin fam miliyan 40.7 a shekara, za a biya shi fam 782,000 a duk mako kafin a cire haraji, kan yarjejeniyar shekara biyar.
Neymar ya ce ''Ya koma daya daga cikin kungiyoyin da suka fi buri a nahiyar Turai''.
''Burin da Paris St-Germain take da shi ne ya bani sha'awar buga wa kungiyar tamaula da kuma kishirwar da take da ita wajen samun nasarori a kwallon kafa''.






