Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Zaɓen Faransa: Macron ya ce zai yi aiki tuƙuru don haɗa kan ƴan ƙasar
Emmanuel Macron ya ce zai yi kokarin hada kan Faransa bayan an sake zabarsa a matsayin shugaban kasa a karo na biyu.
A jawabinsa na nasarar da ya yi ga taron jama'ar da suka taru a hasumiyar Eiffel da ke birnin Paris, ya amince da cewa mutane da dama sun kaurace wa ko kuma sun zabe shi ne kawai don hana abokiyar hamayyar sa Marine Le Pen mai tsatsauran ra'ayi shiga fadar Elysee.
Mista Macron, wanda ya zamo shugaban Faransa na farko da aka zaba a wa'adi na biyu cikin shekaru ashirin, ya yi alkawarin samar da sabbin tsare-tsare, tare da mayar da hankali kan matasa da muhalli, ya kara da cewa ba za a bar kowa a baya ba.
Tazarar da Mista Macron ya samu a zaben na ranar Lahadi ta kai kashi goma sha bakwai bisa dari kan abokiyar hamayyarsa.
Wannan shi ne karo na uku da Marine Le Pen ta sha kaye a zaben shugaban kasa, kuma na biyu a jere bayan Emmanuel Macron.
Ta ce girman kuri'arta, kusan kashi arba'in da biyu cikin dari ya nuna cewa adawa da Mista Macron na ƙara ƙarfi sosai.
Ta sha alwashin ci gaba da yakar shugaban kasar a zaben 'yan majalisar dokoki da za a yi a watan Yuni.
Bayan sanar da sakamakon, an yi zanga-zanga a garuruwa da birane da dama na Faransa, a birnin Paris, 'yan sanda sun yi arangama da magoya bayan Madam Le Pen a Place de la Republique da ke tsakiyar birnin Paris.