Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kano Pillars ta doke Gombe United a wasan mako na 19 a gasar Firimiya
Kano Pillars ta yi nasarar doke Gombe United da ci 3-1 a wasan mako na 19 a gasar Firimiyar Najeriya da suka fafata ranar Lahadi.
Pillar ta fara cin kwallo ta hannun Ifeanyi Eze a minti na 12 da fara wasa daga baya ya kara na biyu saura minti bakwai su je hutu.
Gombe ta zare daya ta hannun Yusuf Abdulazeez, daga baya Rabiu Ali ya kara na uku saura minti biyu a tashi daga wasan.
Da wannan sakamakon Pillars ta yi sama zuwa mataki na 11 a teburi da maki 24.
Rivers United ce ta daya a kan teburi mai maki 42, yayin da Plateau United ke biye da ita da tazarar maki daya tsakani.
Sauran sakamakon wasannin da aka buga ranar Lahadi a Firimiya:
- Remo Stars 3-0 Kwara United
- Plateau Utd 2-0 Sunshine Stars
- Wikki 0-0 Enyimba
- Rivers Utd 4-1 Akwa Utd