Cameroon 4-1 Ethiopia: Kafar Kamaru daya ta kai zagaye na biyu a Afcon

Tawagar Kamaru ta doke ta Habasha da ci 4-1 a wasa na biyu na rukunin farko da suka kara ranar Alhamis a gasar cin kofin nahiyar Afirka a Yaounde.

Minti hudu da fara kwallo Habasha ta ci Kamaru ta hannun Dawa Hotessa daga baya Karl Toko Ekambi ya farke.

Bayan da wasan ya nutsa kyaftin din Kamaru Vincent Aboubakar ya ci na biyu, sannan ya kara na uku daga baya Karl Toko Ekambi ya ci na hudu kuma na biyu da ya zura a raga kenan.

Da wannan sakamakon Kamaru ta hada maki shida a wasa biyu da cin kwallo shida aka zura mata biyu a raga.

Wasa na biyu a rukunin farko za a yi ne tsakanin Cape Verde da Burkina Faso ranar Alhamis.

A wasan farko Cape Verde ta hada maki uku, bayan da ta ci Habasha 1-0, haka kuma a ranar ce Burkina Faso ta yi rashin nasara a hannun mai masaukin baki Kamaru da ci 2-1.

Ranar Litinin Monday 17 ga watan Janairu ake sa buga wasanin karshe a rukunin farko da fafatawa tsakanin Burkina Faso da Ethiopia a Kouekong Stadium.

A kuma lokacin mai masukin baki Kamaru za ta kece raini da Cape Verde a Paul Biya Stadium.