Kasuwar 'yan kwallo: Lewandowski da Fernandes da Koulibaly da Rudiger da Kounde da kuma Wilshere

Liverpool tana daga cikin masu son yin zawarcin dan kwallon Poland, Robert Lewandowski, mai shekara 33, wanda ake sa ran zai bar Bayern Munich a karshen kakar bana. (Fichajes, in Spanish)

Manchester United na ci gaba da tattaunawa da Bruno Fernandes tun cikin watan Yuli. Mai shekara 27 ya ce yana son ci gaba da taka leda a Old Trafford, kuma United ta dauki batun tsawaita zamansa da Paul Pogba da mahimmanci. (Fabrizio Romano via Twitter)

United na fatan kulla ciniki da Napoli kan daukar kyaftin din Senegal, Kalidou Koulibaly a karshen kakar bana, sai dai kungiyar ba za ta taya dan wasan kan fam miliyan 34 da aka gindayawa duk mai son daukarsa ba. (Corriere dello Sport via Express)

Liverpool tana son sayen dan wasa a watan Janairu shi ne dan kasar Jamus Karim Adeyemi, mai shekara 19, daga kungiyar Red Bull Salzburg. (Mundo Deportivo, in Spanish)

Chelsea za ta iya sayar da Antonio Rudiger domin ta samu kudin daukar dan kwallon Sevilla, mai tsaron baya Jules Kounde. Kungiyar PSG da kuma Real Madrid na son sayen dan kwallon da Thomas Tuchel ke son kai wa Stamford Bridge. (Football 365)

Dan kwallon Inter Milan Lautaro Martinez an bayar da rahoton na daf da sa hannu kan sabuwar yarjejeniya a kungiyar Italiya. Hakan na nufin sai Arsenal da Tottenham sun fitar da kudi mai tsoka kafin su samu damar sayen dan wasan. (Gazzetta dello Sport, in Italian)

Tsohon dan kwallon Arsenal Jack Wilshere baya neman kulla yarjejeniyar buga wa Arsenal wasa kan tsarin iya wasanka iya albashinka a Emirates, bayan da Mikel Arteta ya bashi damar yin atisaye a Gunners. Tsohon dan wasan tawagar Ingila bai da kungiya tun bayan da ya bar Bournemouth a karshen kakar da ta kare. (Metro)