Lionel Messi: Dan wasan Argentina ya shiga gaban Pele a tarihin zura kwallo a Kudancin Amurka

Lionel Messi and other Argentina players celebrate with the Copa America trophy

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Messi yana haskakawa sosai a tawagar Argentina

Lionel Messi ya shiga gaban Pele a matsayin dan wasan da ya fi kowa zura kwallo a yankin Kudancin Amurka, bayan da ya ci kwallo uku a wasan da Argentina ta doke Bolivia da ci uku da nema.

Hakan ya nuna cewa Messi ya zura kwallo 79 a wasanni 153 da ya buga wa Argentina.

Shi kuwa fitaccen dan kwallon Brazil, Pele, ya ci kwallo 77 ne a cikin wasanni 92 da ya buga wa kasarsa.

Bayan an tashi wasan na share-fagen buga gasar cin Kofin Duniya, Messi tare da sauran abokan wasansa sun yi murnar wannan nasarar.

Argentina ce kasa ta biyu a yayin da Brazil ke ta farko a rukunin kasashen Kudancin Amurka da ke kokarin tsallakewa zuwa gasar cin Kofin Duniya a shekara ta 2022.