Cristiano Ronaldo: Kocin Real Madrid ya ce ba batun sake daukar Ronaldo

Mai horar da Real Madrid, Carlo Ancelotti ya yi watsi da batun da ake cewar zai sake aiki tare da Cristiano Ronaldo a Real Madrid.

Dan kwallon Juventus, mai shekara 36, yana da sauran kwantiragin wata 10 a Turin, wanda ake alakanta shi da komawa Paris Saint-Germain ko kuma Manchester City.

Hakan ne ya sa Ancelotti ya bayyana a kafar sa ta sada zumunta ta Twitter ranar Talata cewar ba za su sake daukar Ronaldo ba.

"Cristiano zakakurin dan wasan Real Madrid ne, kuma ina kaunar sa ina jinjina masa. Amma ban taba tunanin sake daukarsa ba.'' in ji Ancelotti.

Ronaldo ya koma Real daga Manchester United a Yulin 2009, wanda ya ci wa kungiyar Sifaniya kwallo 450 a karawa 438 a kaka tara da ya yi, daga nan ya koma Juventus kan fam miliyan 99.2

A lokacin da Ronaldo ya taka leda a Real ya lashe Champions League hudu da La Liga biyu, kuma daya daga kofin Zakarun Turai da ya dauka a lokacin Carlo Ancelotti ne a kungiyar.

An ta yada jita-jitar makomar Ronald tun bayan da Lionel Messi ya bar Barcelona, kungiyar da ya yi shekara 21 ya koma Paris St Germain kan yarjejeniyar shekarar biyu.