Lionel Messi: Paris St-Germain na tattaunawa da dan wasan Argentina bayan barin Barcelona

Kylian Mbappe and Lionel Messi

Asalin hoton, Getty Images

Paris St-Germain na tattaunawa da wakilan Lionel Messi kan komawa buga Ligue 1, bayan da ya bar Barcelona.

An shaidawa BBC cewar wakilan Messi sun tuntubi PSG tun ranar Alhamis, bayan da Barcelona ba za ta iya biyan Messi albashi ba, sakamakon matsin tattalin arziki da take fuskanta.

Bangarorin biyu sun ci gaba da tattaunawa ranar Asabar, ana kuma sa ran za su cimma matsaya nan ba da dadewa ba.

Messi mai shekara 34 bai da wata kungiya tun bayan da yarjejeniyarsa ya kare a Barcelona a farkon watan Yuli.

Tun farko ya amince zai ci gaba da zama a Camp Nou kan yarjejeniyar kaka biyar da rage rabin albashinsa, amma Barcelona ba ta da kudin da za ta bai wa kyaftin din Argentina.

Tsohon kyaftin din Barcelona ya ci kwallo 672 a kungiyar da lashe La Liga 10 da Champions League hudu da Copa del Rey bakwai da kyautar Ballon d'Or shida.

Messi zai ji dadin taka leda a PSG ganin cewar yana da abokai da ya sani a kungiyar yanzu haka.

Neymar ya buga wasa a Barcelona daga 2013 zuwa 2017 daga baya ya koma PSG kan fam miliyan 200 a matakin wanda aka saya mafi tsada a duniya, kuma abokin kyaftin din Argentina ne.

Messi on holiday this month with PSG's Neymar, Paredes, Di Maria and Verrati

Asalin hoton, Neymar

Bayanan hoto, Messi a lokacin hutu tare da abokanai da suka hada da 'yan kwallon PSG, Neymar da Paredes da Di Maria da kuma Verrati

An dauki hoton Messi da Neymar da 'yan wasan Argentina Angel di Maria da Leandro Paredes da dan kwallon PSG, Marco Verrati a lokacin hutu a farkon watan nan.

Cinikin zai yi daidai da dokar kashe kudi iya samunka, saboda PSG ta dauki 'yan wasa a bana wadanda kwantiraginsu ya kare kamar su Sergio Ramos da Georginio Wijnaldum da kuma mai tsaron raga, Gianluigi Donnarumma, sannan ta sayi Achraf Hakimi daga Inter Milan.

Graphic showing Paris St-Germain's possible starting line-up for 2020-21

Asalin hoton, BBC Sport

Bayanan hoto, Yadda ake sa ran PSG za take saka 'yan wasa idan Messi ya koma kungiyar