Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Odion Ighalo: Dan wasan Najeriya ya kawo karshen zamansa a Manchester United
Dan kwallon Najeriya, Odion Ighalo ya bayyana cewa 'mafarkinsa ya zo karshe' saboda zai bar Manchester United bayan shafe shekara daya yana murza leda a kulob din a matsayin aro.
Dan wasan, mai shekaru 31, ya zura kwallo biyar a wasa 23 da ya buga wa United tun bayan da aka dauko shi daga kungiyar Shanghai Shenhua ta China.
Ighalo ya ce: "Ina godiya da wannan damar kuma ba zan taba mantawa ba".
A sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter Ighalo ya ce " Zan ci gaba da kasancewa mai goyon bayan Manchester United har abada".
A kakar wasa ta bana, Ighalo ya murza leda ne kawai na minti tara a gasar firemiya kuma ya koma cin benci ne bayan da aka dauko Edinson Cavani a cikin watan Oktoba.