Kasuwar cinakayyar yan wasa: Makomar Sancho, Ramos, Mbappe, Neymar,Mustafi da Traore

Har yanzu Mancheser United na nan kan bakanta na ci gaba da zawarcin dan wasan gaban Borussia Dortmund Jadon Sancho. (90 min).

PSG za ta taya mai tsaron bayan Real Madrid da Sfaniya Sergio Ramos. Ramos na da damar kulla yarjejeniya da wata kungiya daga ranar 1 ga watan Janairu. (AS)

A wata mai kama da haka PSG na kokarin tsawaita kwantiragin dan wasan gabanta Kylian Mbappe mai shekaru 21 da kuma dan wasan Brazil Neymar mai shekaru 28. (Goal).

Kungiyoyin Everton da Tottenham na sha'awar kawo dan wasan gaban Napoli Arkadiusz Milik wanda a ke saran kudinsa ya kai fam miliyan 10 a kasuwar cinikayyar yan wasa ta watan Janairu. (Sun)

Celtic na sha'awar dauko mai tsaron gidan Manchester United Dean Henderson mai shekaru 23 a matsayin aro. (90 min).

A Sfaniya kuwa Barcelona ce ke tunanin dauko mai tsaron bayan Arsenal da Jamus Shkodran Mustafi. Mustafi mai shekaru 28 shi ne wanda Barca ta yi kwanto da shi matsawar ta kasa sayen mai tsaron bayan Chelsea Antonio Rudiger. (Express)

Dan wasan gaban Wolves da Sfaniya Adama Traore mai shekaru 24 ya ce ba a fara wasa da shi ne kawai saboda ya ki tsawaita zamansa a kungiyar. Yanzu haka yana da yarjejeniya da Wolves har zuwa shekarar 2023. (The Athletic).

Tsohon mai tsaron bayan Chelsea da Ingila John Terry na daga cikin masu neman aikin horar da kungiyar Derby County. (Mail)

Manchester United na neman mai tsaron bayan Sporting Braga David Carmo mai shekara 20. (The Athletic - subscription required)

Akwai yiwuwar Chelsea za ta sayar da wasu daga cikin yan wasanta don hada fam miliyan 67 na sayen dan wasan West Ham Declan Rice mai shekaru 21. (Express)