Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Alex Telles ya kara kamuwa da cutar korona karo na biyu
Manchester United na fatan Alex Telles zai buga mata karawar da West Brom ranar Asabar, duk da sake kamuwa da cutar korona karo na biyu da ya yi.
Mai tsaron bayan, mai shekara 27 ya kamu da annobar a lokacin da ya je buga wa Brazil tamaula, ba zai buga wasan da za ta yi da Uruguay ranar Talata ba.
United za ta auna dan wasan da zarar ya koma Ingila don fayyace ko zai iya buga mata gasar Premier League.
Ranar Asabar United za ta karbi bakuncin West Brom a gasar cin kofin Premier League.
United tana ta 14 a kasan teburin Premier da maki 10, ita kuwa West Brom tana ta 18 da maki uku kacal.
Telles ya buga ya United karawa daya shi ne wanda ta doke Paris St Germain a Champions League a Faransa ranar 20 ga watan Oktoba.
Tun daga nan bai sake yin wasa ba, sakamakon kamuwa da cutar korona.
Brazil za ta ziyarci Uruguay domin buga karawa ta hudu ta cikin rukuni a wasannin neman shiga gasar cin kofin duniya da za a yi a Qatar.
Telles ya koma Manchester United daga Porto kan kwantiragin shekara hudu a watan Oktoba.