Javier Mascherano ya bar sana'ar kwallon kafa

Tsohon dan wasan Liverpool, Javier Mascherano ya sanar da yin ritaya daga buga kwallon kafa.

Dan wasan tawagar kwallon kafa ta Argentina ya sanar da rataye takalmansa na tamaula, bayan da aka doke kungiyarsa Estudiantes.

Mai shekara 36 ya buga tamaula a River Plate da Corinthians da West Ham da Liverpool da Barcelona da kuma Hebei China Fortune.

Mascherano ya lashe kofi daya a gasar Argentina da kuma daya a ta Brazil da wadanda ya ci da yawa a Barcelona.

Mai tsaron bayan ya dauki La Liga biyar a Spaniya da Copa del Rey biyar da Champions League biyu da UEFA Super Cup biyu.

Haka kuma ya lashe kofin zakarun nahiyoyin duniya wato World Club Cup biyu da Supercopa Espana uku a Barcelona.

Yana kuma cikin 'yan wasan tawagar Argentina da su kai wasan karshe karo uku a jere a Gasar kofin duniya da Copa America.

Ya daina buga wa Argentina wasa a 2018 wacce ya yi wa karawa 147 da buga Gasar kofin duniya hudu.