Lionel Messi ya fara yi wa Barca wasa ranar 16 ga Nuwamba 2003

Litinin 16 ga watan Nuwamba ita ce ranar da Barcelona ta fara sa Lionel Messi a wasan sada zumunta da ta yi da Porto.

Dan wasan tawagar kwallon kafar Argentina ya fara yi wa Barcelona tamaula yana da shekara 16 da haihuwa ranar 16 ga Nuwambar 2003.

Ya kuma fara wasa ne a karkashin koci, Frank Rijkaard a filin wasa na Do Drago, inda Barcelona ta yi rashin nasara da ci 2-0.

Messi ya shiga wasan sada zumuntar a minti na 71 dauke da lamba 14, ya kuma canji Fernando Navarro a fafatawar.

Tun daga nan ne kuma Messi ya ci gaba da sa kwazo da ya zama daya daga cikin fitattun 'yan kwallo a duniya.

Wasu bajintar da Messi ya yi a Barcelona:

Kawo yanzu Messi ya buga wa Barcelona wasa 741 ya ci kwallo 640 ya kuma bayar da 278 aka zura a raga.

Kofin La Liga 10

2004/05 da 2005/06 da 2008/09 da 2009/10 da 2010/11 da 2012/13 da 2014/15 da 2015/16 da 2017/18 da kuma 2018/19

Champions League uku

2005/06 da 2008/09 da 2010/11 da kuma 2014/15

Copa del Rey shida

2008/09 da 2011/12 da 2014/15 da 2015/16 da 2016/17 da kuma 2017/18

Club World Cup uku

2009/10 da 2011/12 da kuma 2015/16

European Super Cup uku

2009/10 da 2011/12 da kuma 2015/16

Spanish Super Cup takwas

2005/06 da 2006/07 da 2009/10 da 2010/11 da 2011/12 da 2013/14 da 2016/17 da kuma 2018/19

FIFA Ballon d'Or guda shida

2009 da 2010 da 2011 da 2012 da 2015 da kuma 2019

FIFA World Cup Golden Ball

2014

FIFA World Player

2009

Golden Shoe shida

2009/10 da 2011/12 da 2012/13 da 2016/17 da 2017/18 da kuma 2018/19

Best Player in Europe

2010/11 da 2014/15

La Liga Top Scorer bakwai

2009/10 da 2011/12 da 2012/13 da 2016/17 da 2017/18 da 2018/19 da kuma 2019/20

Champions League Top Scorer shida

2008/09 da 2009/10 da 2010/11 da 2011/12 da 2014/15 da kuma 2018/19