Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Marco Asensio: Ya buga wa Real Madrid wasa 100 a Gasar La Liga
Ranar Lahadi Real Madrid ta yi rashin nasara da ci 4-1 a gidan Valencia a wasan mako na tara a Gasar La Liga.
Marco Asensio ya buga fafatawar a gidan Valencia, kuma wasa na 100 da ya yi wa kungiyar a Gasar cin Kofin La Liga kenan, ya kuma zura kwallo 13 a tarihi.
Dan kwallon wanda yake kaka ta biyar a Real Madrid an ci wasa 65 da shi daga 100 da ya buga a gasar ta kasar Spaniya.
A shekara biyar da ya yi a kungiyar ya daga kofi 11 ciki har da European Cup biyu da Club World Cup uku da Uefa Super Cup biyu.
Sauran kofunan da dan wasan ya lashe a Madrid sun hada da La Liga daya da kuma Spanish Super Cups.
A kakar farko da ya fara buga wa Real tamaula, Asensia ya yi wasan La Liga 23, inda aka ci 19 da shi da canjaras uku da rashin nasara daya, ya zura kwallo uku a raga a kakar.
A kakar nan ta 2020/21, Asensio ya buga wasa shida a La Liga, an kuma yi nasara da shi a karawa hudu da rashin nasara a fafata biyu.
A kakar 2017/18 ita ce dan kwallon ya buga La Liga da yawa har 32, ya kuma ci kwallo shida.