Kasuwar 'yan ƙwallon ƙafa: Makomar Pochettino, Ozil, Garcia, Malen, Kabak

Tsohon kocin Tottenham Mauricio Pochettino da kuma kocin tawagar ko-ta-kwana taReal Madrid Raul na cikin mutanen da ake sa ran dauka domin maye gurbin Zinedine Zidane idan kungiyar ta kore shi. (AS)

Dan wasanArsenal Mesut Ozil zai iya tafiya Amurka inda aka ce DC United na son dan wasan mai shekara 32. (Sun)

Kocin Manchester City Pep Guardiola yana fatan "rarrashin" dan wasan Sufaniya Eric Garcia, mai shekara 19, domin ya tsawaita zamansa. (Independent)

Arsenal na duba yiwuwar kulla yarjejeniya domin sake daukar Donyell Malen, mai shekara 21, daga PSV Eindhoven, shekara uku bayan sun sayar da dan wasan na Netherlands daga tawagarsu ta matasa a kan £540,000. (Soccernews, via Star)

Liverpool za ta iya mayar da hankalinta kan dan wasan Schalke dan kasar Turkiyya Ozan Kabak, mai shekara 20, a yayin da suke neman wanda zai maye gurbin dan wasan Netherlands da ya ji rauni Virgil van Dijk, mai shekara 29. (Sport Media Set, via Sport Witness)

Dan wasanBarcelona dan yankin Catalan Gerard Pique, mai shekara 33, ya amince a rage albashinsa da kaso 50 zuwa karshen kakar wasa ta bana, saboda mawuyacin halin tattalin arziki da annobar korona ta jefa kungiyar a ciki. (Sport)

Dan wasan Sufaniya Sergio Reguilon, mai shekara 23, ya ce tsohon kocinReal Madrid Jose Mourinho yana cikin manyan dalilan da suka sanya ya tafi Tottenham. (Sky Sports)

Arsenal ta soma gwada dan gidan tsohon dan wasan Netherlands Dennis Bergkamp. Mitchel Bergkamp, mai shekara 22, ya kwashe mako daya yana atisaye a London Colney inda yake samun kulawar Steve Bould da ke kula da masu murza leda a rukunin 'yan kasa da shekara 23. (Goal)

Dan wasan Manchester United Aaron Wan-Bissaka yana son samun gurbi a tawagar Ingila kuma ba zai sauya kasa ba don wakiltar Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo. (Telegraph - subscription required)

Dan wasan da Chelsea ta dauka a bazaraHakim Ziyech, dan kasar Morocco mai shekara 27, ya ce ya tafi Stamford Bridge ne domin "samun damar murza leda mai kyau da kuma cin kwallaye". (London Evening Standard)

Tsohon dan wasan Scotland Darren Fletcher, mai shekara 36, ya koma Manchester United domin taka rawa ta mai horas da 'yan wasa. (Manchester Evening News)