Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Rapid Vienna 1-2 Arsenal: Gunners ta fara kakar Europa da kafar dama
Arsenal ta yi nasara da ci 2-1 a gidan Rapid Vienna a wasan farko a rukuni na biyu a Gasar Zakarun Turai ta Europa League da suka kara ranar Alhamis.
Mai masaukin baki ce ta fara cin kwallo ta hannun Taxiarchis Founta, bayan da mai tsaron ragar Arsenal ya yi kokarin bayar da kwallo aka tare aka kuma ci Gunners.
Mai tsaron baya, David Luiz shi ne ya farkewa Arsenal kwallo, sannan Kyaftin Pierre-Emerick Aubameyang ya ci na biyu da ya bai wa Gunners damar hada maki uku a wasan farko.
Golan na Arsenal, Leno ya kara yin kuskure a karo na biyu, bayan da ya cire kwallo sai kawai ta je gurin Fountas kai tsaye, wanda ya yi kokari ya ci, amma golan ya sa kwazo.
Arsenal ta saka sabon dan wasan da ta saya a bana fam miliyan 45 wato Thomas Partey, ya kuma taka rawar gani da nuna cewar ba a yi zaben tumun dare ba.
Leno ya kasa kwantar da hankalinsa a karawar domin akwai kwallon da ya buga ta bugi bayan Luiz sai Fountas ya karba, sai dai ya kasa amfana da damar da ya samu.
Arsenal za ta karbi bakuncin Dundalk kungiyar kwallon kafa daga Ireland ranar 29 ga watan Oktoba a Emirates a wasan gaba na rukuni na biyu.
Kafin nan Leicester City za ta ziyarci Gunners ranar 25 ga watan Oktoba domin buga Gasar Premier League.
Wasu sakamakon wasannin da aka buga a Gasar Europa League:
- BSC Young Boys 1 : 2 Roma
- CSKA Sofia 0 : 2 CFR Cluj
- Dundalk 1 : 2 Molde FK
- Bayer 04 Leverkusen 6 : 2 Nice
- Hapoel Beer Sheva 3 : 1 Slavia Prague
- PSV Eindhoven 1 : 2 Granada
- PAOK Salonique 1 : 1 Omonia Nicosia
- SSC Napoli 0 : 1 AZ Alkmaar
- HNK Rijeka 0 : 1 Real Sociedad
- Standard de Liege 0 : 2 Glasgow Rangers
- KKS Lech Poznan 2 : 4 Benfica