Kasuwar 'yan ƙwallon ƙafa: Makomar White, Mbappe, Greenwood, Rose, Welbeck, Deeney

Asalin hoton, Getty Images
Mai yiwuwa Brighton ta nemi a biya ta akalla £50m kan dan wasanta Ben White idan Liverpool tana so ta maye gurbin dan wasan Netherlands wanda ya ji rauni Virgil van Dijk, mai shekara 29, da dan wasan na Ingila mai shekara 23 a watan Janairu. (Sun)
Dan wasan Faransa Kylian Mbappe, mai shekara 21, zai iya barin Paris St-Germain zuwa Liverpool ko Real Madrid a bazara mai zuwa. (Le Parisien - in French)
Manchester United ta ja kunnen dan wasanta Mason Greenwood, mai shekara 19, kan zuwa wasa latti. (Mail)
Tottenham na shirin tattaunawa domin bai wa dan wasan Ingila Danny Rose, mai shekara 30, damar barin kungiyar nan ba da jimawa ba. (Football Insider)
Dan wasan Ingila Danny Welbeck, mai shekara 29, ya yi watsi da tayin £140,000 duk mako daga wurin kungiyar Turkiyyya da ke buga gasar Super Lig - wadda aka yi amannar cewa Fenerbahce ce - domin ya ci gaba da zama a Brighton. (Sun)
Kyaftin na Watford Troy Deeney, mai shekara 32, ya dage cewa yana nan kan ganiyarsa a yayin da rahotanni ke cewa Tottenham da wasu kungiyoyin Firimiya na zawarcinsa. (Talksport)
Dan wasan Portugal Gedson Fernandes, mai shekara 21, wanda ke zaman aro a Tottenham daga Benfica, mai yiwuwa zai gaggauta komawa kungiyarsa a watan Janairu bayan ya gaza tabuka komai a Lilywhites. (RTP 3, via Sun)
Dan wasan Uruguay Lucas Torreira, mai shekara 24, ba shi da niyyar komawa Arsenal kuma yana son zaman aron da yake yi a Atletico Madrid ya zama na dindindin. (Ovacion Digital, via Star)
KocinAston Villa Dean Smith ya ce ba su tattauna kan sayen dan wasan da suka aro daga Chelsea Ross Barkley,mai shekara 26, ba. (Birmingham Mail)
Barcelona ta gaggayci 'yan wasanta domin tattaunawa kan rage albashin ma'aikatanta, sai dai ana ganin 'yan wasan ba za su halarci taron ba saboda suna so a yi tattaaunawarsu daban da ta sauran ma'aikata. (Goal)
Dan wasanChelsea dan kasar Faransa Olivier Giroud, mai shekara 34, ya ce tattaunawar da ya kwashe kwana uku yana yi da koci Frank Lampard a watan Janairu ce ta sanya shi zama a kungiyar kuma ya ce yana cike da farin ciki a Stamford Bridge. (Onze Mondial, via Express).











