Manchester United ta yi hasarar fam miliyan 70 sakamakon cutar korona

Asalin hoton, Getty Images
Manchester United ta yi hasarar kudin shiga da ta yi hasashen samu da ya kai fam miliyan 70 tsakanin zuwa 30 ga watan Yunin 2020, sakamakon cutar korona.
Kudin sun hada da ƙididdiga ta 2019-20, tun daga lokacin da aka dakatar da wasanni a Ingila, sakamakon bullar annobar.
Baki ɗaya kudin shiga ya ragu a United zuwa kaso 18.8 cikin 100 daga fam miliyan 627.1 zuwa fam miliyan 509, amma wasu daga ciki saboda rashin zuwan kungiyar Champions League.
A bara United ta yi hasashen cewar za ta samu kudin shiga da zai kai fam miliyan 580.
Kungiyar ta Old Trafford ta kashe fam miliyan 75 wajen sayo sabbin 'yan kwallo a kakar bana.
United ta samu ribar fam miliyan 18.9 a kakar 2018-18, sai dai ta yi hasarar fam miliyan 23.2 a 'yan shekarun nan.
An dakatar da dukkan wasanni a Ingila a cikin watan Maris, don gudun yaɗa cutar korona daga baya aka ci gaba da wasanni ba 'yan kallo tun daga watan Yuni.
United ta fara kakar bana ta Champions League da ƙafar dama, bayan da ta je ta doke Paris St-Germain da ci 2-1 ranar Talata.
Ranar Asabar United za ta karbi bakuncin Chelsea a gasar Premier League a Old Trafford.










