Kasuwar 'yan ƙwallon ƙafa: Makomar Ozil, Sarr, Keane, Barcelona, Premier League

Asalin hoton, Getty Images
KocinArsenal Mikel Arteta ya shaida wa Mesut Ozil, mai shekara 32, cewa ya ba shi wata biyu domin ya nuna musu cewa zai iya yin abun da suke so. Dan wasan bai murza leda ba tun ranar 7 ga watan Maris. (Express)
Watford ta ki amincewa da £25m da Crystal Palace ta mika mata don daukar dan wasan Senegal Ismaila Sarr, mai shekara 22. (Mail)
'Yan wasanBarcelona sun ki amincewa da bukatar da shugaban kungiyar Josep Maria Bartomeu ya gabatar ta rage musu albashi. (Marca)
Kocin Leicester Brendan Rodgers ya ce har yanzu Islam Slimani, mai shekara 32, yana cikin tsare-tsarensa. Dan wasan na Algeria bai buga wa kungiyar tamaula ba tun watan Janairun 2018. (Telegraph - subscription required)
Tsohon dan wasan da ke buga gasar Firimiyar Ingila dan yankin Jamhuriyar Ireland Robbie Keane, mai shekara 40, zai tafi LA Galaxy domin zama sabon kocin kungiyar. (Sun)
An gargadi Hukumar Gasar Firimiyar Ingila cewa gwamnati za ta iya cin ta tara kan yadda ake watsa wasannin kwallon kafa idan ta gaza inganta tsarinta. (Telegraph - subscription required)






