Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
AC Milan ta dauki aron Diogo Dalot daga Manchester United
AC Milan ta dauki aron dan kwallon tawagar Portugal, Diogo Dalot mai tsaron baya a Manchester United.
United ta sayi dan kwallon kan fam miliyan 19 a Yunin 2018 daga Porto, inda dan wasa mai shekara 21 ya saka hannu kan yarjejeniyar shekara biyar da Old Trafford.
Wasa daya Dalot ya buga wa United a bana shi ne a Caraboa Cup da suka doke Brighton.
Kwallon da dan wasan ya buga ne aka samu fenatin da Marcus Rashford ya buga ya ci da aka fitar da Paris St-Germain daga Champions League a Maris din 2019.
Lokacin da United ta dauki dan kwallon, Jose Mourinho ya kwatanta matashin dan wasan a matakin babu kamarsa a nahiyar Turai cikin tsaransa.
Ya buga wasa 23 a kakar farko da ya fara yi wa United kwallo, a kaka ta gaba kuwa da kungiyar ta dauko Aaron Wan-Bissaka, karawa 11 ya yi mata.