Kasuwar 'yan ƙwallon ƙafa: Makomar Hudson-Odoi, Dembele, Sancho, Alonso, Skriniar

Asalin hoton, Getty Images
Bayern Munich tana tattaunawa da Chelsea a kan karbar aron dan wasan Ingila mai shekara 19 Callum Hudson-Odoi tsawo kakar wasa guda. (Sport Bild, via Mail)
Dan wasan Faransa Ousmane Dembele, mai shekara 23, ya sauya matsayi kan tafiya Manchester United - amma kungiyarsa Barcelona ba ta hana shi tafiya ba. (L'Equipe via Mirror)
Dan wasan tsakiyarManchester United Paul Pogba, mai shekara 27, ya kira dan kasarsa ta Faransa Dembele domin ya roke shi ya tafi Old Trafford. (Mundo Deportivo - in Spanish)
KocinManchester United Ole Gunnar Solskjaer ya gwammace sayar da Daniel James, mai shekara 22, domin ya samu kudin sayen dan wasan Borussia Dortmund da Ingila mai shekara 20, Jadon Sancho. Sai dai har yanzu Solskjaer bai gamsar da kungiyar ta sayar da dan wasan na Wales ba. (ESPN)
Leeds United ta farfado da shirinta na zawarcin James inda za ta bai wa Manchester United £25m. (Football Insider)
Chelsea ta shaida waInter Milan cewa ta gwammace ta sayar da dan wasan Sufaniya Marcos Alonso baki daya bayan kungiyar da ke buga gasar Serie A ta nemi aron dan wasan mai shekara 29. (Goal)
Dan wasanManchester United Diogo Dalot, mai shekara 21, yana tattaunawa da AC Milan - amma Roma tana son dauko dan kasar ta Portugal a wani bangare na yarjejeniya kan dan wasan United dan kasar Ingila Chris Smalling, mai shekara 30. (Sun)
Dan wasan Arsenal dan kasar Uruguay Lucas Torreira, mai shekara 24, ya isa kasar Sufaniya inda za a duba lafiyarsa a Atletico Madrid ranar Asabar kafin ya kammala yarjejeniyar zaman aro na kakar wasa daya, da kuma zabin sayensa kan £18.1m. (AS - in Spanish)
Tottenham za ta sake yunkurin dauko dan wasan Inter dan kasar Slovakia Milan Skriniar, mai shekara 25, a karshen makon nan bayan kammala karbo aron dan wasan Benfica Carlos Vinicius. (Standard)
Bournemouth, Swansea City da Luton Town dukka suna son dauko dan wasan Tottenham da Amurka Cameron Carter-Vickers, mai shekara 22. (Mail)
Arsenal za ta iya tura dan wasan Faransa William Saliba, mai shekara 19, domin zaman aro, a yayin da suka tattauna da Rennes. (Guardian)











