Sadio Mane: Ɗan wasan Liverpool ya killace kansa bayan ya kamu da coronavirus

Asalin hoton, Reuters
Ɗan wasan tsakiya na Liverpool Sadio Mane ya kamu da cutar korona kuma yanzu haka ya killace kansa.
Lamarin na faruwa ne kwana uku bayan kungiyar ta sanar cewa dan wasan tsakiya Thiago Alcantara ya harbu da Covid-19.
Liverpool ta ce dan wasan na Senegal "ya nuna kananan alamomin kamuwa da cutar amma dai yana cike da kazar-kazar".
Mane, mai shekara 28, ya murza leda a wasan da Liverpool ta doke Arsenal da ci 3-1 ranar Litinin amma ba a sanya shi a tawagar da ta sha kashi a bugun fenareti a gasar cin Kofin EFL ranar Alhamis ba.
Sanarwar da kungiyar ta wallafa a shafinta na intanet ta kara da cewa: Kamar yadda ya faru da Thiago Alcantara, Liverpool za ta ci gaba da bin ka'idojin kare kai daga kamuwa da Covid-19 kuma Mane zai killace kansa tsawon lokacin da aka bukata."
Mane, wanda ya zura kwallo uku a wasannin da Anfield ta buga a kakar bana, yanzu ba zai fafata a ledar da za su murza da Aston Villa ba a gasar Premier ranar Lahadi gabanin tafiya hutu.
Wasan farko da kungiyar za ta buga bayan hutu shi ne wanda za ta fafata a wasan hamayya na Merseyside a Everton ranar 17 ga watan Oktoba.
Ranar Litinin, hukumar gasar Premier League announced 10 people ta bayyana cewa mutum 10 ne suka kamu da cutar korona a gwaje-gwajen baya bayan nan da aka yi a kansu, kuma wannan shi ne adadi mafi girma tun da aka soma kakar bana.











