Alvaro Morata: Juventus ta sake daukar aron dan wasan Atletico Madrid

Juventus ta kammala daukar aron dan wasan Atletico Madrid, Alvaro Morata da zai buga mata tamaula tun daga bana.

Dan kwallon tawagar Spaniya, mai shekara 27, ya saka hannu kan yarjejeniyar da za ta kare a karshen kakar 2020-21.

Cikin kunshin kwantiragin, Juventus za ta iya tsawaita zaman Morata a kungiyar zuwa shekara daya ko kuma ta saya idan ya taka mata rawar gani.

Juventus za ta biya Atletico fam miliyan 9.2 a duk zaman da ya yi a kungiyar a matakin aro.

Ranar 1 ga watan Yuli, Morata ya sa hannu kan yarjejeniya a Atletico, bayan wasannin aro da ya buga a Italiya.

Dan kwallon ya buga wa Juventus wasa tsakanin 2014 da 2016, inda kungiyar ta lashe lashe Serie A biyu.

Kungiyar ta Italiya za ta iya sayen dan wasan kan fam miliyan 41 a karshen kakar bana, ko kuma fam miliyan 32 a kaka ta biyu idan ya kammala buga mata wasannin aro.

Morata ya buga wa Real Madrid da Chelsea tamaula, daga nan ya koma Atletico buga mata tamaula aro kan yarjejeniyar wata 18.

Juventus na fatan lashe kofin Serie A na 10 a jere, ta kuma fara kakar bana da kafar dama, bayan da ta doke Sampdoria 3-0 ranar Lahadi.