Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Sancho, Sarr, Bellerin, Mendy, Giroud, Hudson-Odoi, Tarkowski
Manchester United na duba yiwuwar daina zawarcin dan wasan Borussia Dortmund da Ingila Jadon Sancho, mai shekara 20. (Star)
Liverpool tana so ta yi shigar wuri domin dauko dan wasanWatford da Senegal Ismaila Sarr, mai shekara 22, a watan Janairu. (Football Insider)
Barcelona tana son karbo aron dan wasan Arsenal da Sufaniya Hector Bellerin, mai shekara 25. (Marca - in Spanish)
GolanRennes Edouard Mendy, mai shekara 28, zai je London a karshen mako domin a duba lafiyarsa bayan Chelsea ta amince ta dauki dan wasan naSenegal. (Star)
Dan wasanChelsea da Faransa Olivier Giroud, mai shekara 33, ya yi "mamaki" a kan da jita-jitar da ake yadawa cewa zai tafi Juventus. (Telefoot, via Mail)
Chelsea na duba yiwuwar bayar da aron dan wasan Ingila Callum Hudson-Odoi, mai shekara 19. (90min)
David Moyes ya ce West Ham ba za ta iya biyan farashin da Burnley ta sanya kan dan wasan Ingila James Tarkowski, mai shekara 27 ba. (Football London, via Lancs Live)
Mai yiwuwaTottenham ba za ta dauko dan wasan Napoli da Poland Arkadiusz Milik, mai shekara 26, ba lokacin musayar 'yan kwallo. (Sky Sports)
KocinCrystal Palace Roy Hodgson ya ce ya yi mamaki saboda babu wata kungiya da ta "kwankwasa musu kofa" domin daukar dan wasan Ivory Coast Wilfried Zaha, mai shekara 27. (Standard)
Tattaunawa ta yi nisa kan yunkurin daWest Brom take yi domin dauko dan wasan Watford da Ingila Troy Deeney, mai shekara 32. (Football Insider)
Brighton ta bi sahun kungiyoyin da ke son dauko golanArsenaldan kasar Argentina Emiliano Martinez. Aston Villa ma tana son dauko dan wasan mai shekara 28. (Guardian)
Dan wasan Switzerland Gaetano Berardi, mai shekara 32, yana fatan sabunta kwangilarsa a Leeds United a wannan wata. Kwangilarsa ta kare a karshen kakar wasan da ta wuce kuma yanzu haka yana gefe inda yake jinya. (RSI - in Italian)