Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Kante, Aubameyang, Smalling, Wijnaldum, Rose, Ivanovic
Chelsea ta ki amincewa da tayin da Inter Milan ta yi na daukar dan wasan Faransa da ya lashe Kofin Duniya N'Golo Kante, mai shekara 29, wanda ya hada da musayar dan wasan Croatia Marcelo Brozovic, mai shekara 27. (Guardian)
Dan wasan Arsenaldan kasar Gabon Pierre-Emerick Aubameyang, mai shekara 31, zai sanya hannu kan sabuwar kwangilar shekara uku abin da zai sa ya zama dan wasan da zai fi kowanne dan wasa tsada a kungiyar. (Athletic - subscription required)
Dan wasanManchester United dan kasar Ingila Chris Smalling, mai shekara 30, bai yi atisaye ba a wannan makon a yayin da yake dab da kammala tafiya Roma, inda ya yi zaman aro a kakar wasan da ta wuce. (Telegraph - subscription required)
Dan wasan Liverpool Georginio Wijnaldum, mai shekara 29, ya yi tattaunawa mai armashi da kocin kungiyar Jurgen Klopp a kan makomarsa. Sauran shekara daya kwangilar dan wasan na Netherlands ta kare a Anfield. (Sky Sports)
Dan wasan Tottenham Danny Rose, mai shekara 30, yana dab da barin Gasar Firimiya inda zai tafi Serie A domin murza leda a Genoa.(PA, via Team Talk)
Golan Arsenal dan kasar Argentina Emiliano Martinez, mai shekara 28, ya amince da kwangilar shekara hudu da Aston Villa, wacce zai rika karbar kusan £60,000 duk mako, a yayin da kungiyoyin ke shirin amincewa kan kudin musaya wadanda suka zarta £15m. (Independent)
Dan wasan Manchester United da Brazil Fred, mai shekara 27, ya yi watsi da rahotannin da ke cewa zai iya barin kungiyar domin tafiya Galatasaray a bazarar nan. (Four Four Two)
West Brom na tattaunawa domin dauko tsohon dan wasan Chelsea Branislav Ivanovic, mai shekara 36, bayan ya bar Zenit St Petersburg.(Telegraph - subscription required)
Dan wasan Tanzania Mbwana Samatta, mai shekara 27, zai iya barin Aston Villa watanni takwas kawai bayan ya je kungiyar. (Mail)
Tsohon dan wasan Manchester United Ravel Morrison, mai shekara 27, yana tattaunawa da kungiyoyin kwallon kafar Netherlands Vitesse Arnhem da Utrecht bayan ya bar Sheffield United. (Mail)
Dan wasan Liverpool Ben Woodburn, mai shekara 20, na shirn tafiyaSparta Rotterdam domin yin zaman aron kakar wasa daya. (Standard)