Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kai Havertz: Wane ne ɗan wasan da Chelsea ta sayo a kan £71m daga Bayer Leverkusen?
- Marubuci, Daga Constantin Eckner
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Masanin kwallon kafar Jamus
Ana kiransa da suna "sabon Michael Ballack" kuma ana kallonsa a matsayin dan wasan da zai yi tashe nan gaba.
Kuma, bayan an kwashe tsawon lokaci ana ciniki a kansa wanda ake ganin kamar ba zai kare ba, yanzu dai Kai Havertz ya tafi Chelsea, inda ya zama dan wasa na biyu mafi tsada da suka saya kuma dan wasan na bakwai da suka sayo a kakar wasa ta bana.
Magoya bayan Chelsea za su yi fatan ganin ya taimaka wajen mayar da kungiyar kan ganiyarta, amma me ya sa kungiyar ta amince ta biya kudin da suka kai £71m - ciki har da kudin talla - kan dan wasan mai shekara 21?
Wane ne wannan dan wasa na Jamus?
An haifi Havertz a 1999 kuma an bayyana shi a matsayin dan wasan Jamus mai matukar basira da ba a samu irinsa ba a cikin takwarorinsa.
Dan wasan na tsakiya da ke kai hari ya soma jan hankalin duniya tun yana da shekara 17, inda ya soma murza leda a Bayer Leverkusen a kakar wasa ta 2016-17, kuma tun a wasansa na farko ya nuna cewa watarana zai shahara.
Havertz yana da wata basira ta musamman wadda 'yan wasan da ke saka riga mai lamba 10 suke da ita, ko da yake ba za a ce yana cikinsu ba - tsawonsa kafa 6 da inchi 2 ne, kuma bajintarsa ce ta sa yake iya taka rawa daban-daban.
Yakan buga tamaula a Leverkusen a bangaren dan wasan tsakiya da ke kai hari, da kuma wasan tsakiya, da na dama, kuma a baya bayan nan yana karbar dan wasan gaba. Kocin tawagar Jamus Joachim Low yana gwada shi a wasu bangarorin masu sarkakiya.
Wasu kasar Jamus suna kallonsa a matsayin sabon Michael Ballack. Tsohon dan wasan tsakiyar na Bayern Munich da Chelsea ya taka irin wannan rawa, inda ya rika bai wa maza kashi.
Ko da yake Havertz ba shi da kirar jiki irinta Ballack, amma yana da hazaka irin tasa inda yake iya yin fitowar ba-zata ya zari kwallo ya cilla ta a raga.
Havertz dan wasan zamani ne wanda ya hada abubuwa da dama ciki har da hikimar mika kwallo, da hangen nesa, da nutsuwa a yayin da ake tsaka mai wuya, da kuma yawan motsa jiki. Ba ya yaudara a cikin filin wasa kuma ba ya yin duk abin da zai kawo masa nakasu. Dan wasa ne da ba ya yarda da raini kamar sabon kocinsa Frank Lampard.
Mene ne tarihin Havertz?
An haife shi ne a wani kauye mai suna Mariadorf kuma iyayensa dan sanda ne da kuma lauya, inda ya girma yana kaunar buga wasa a karamar kungiyar Alemannia Aachen.
Ya ja hankalin tawagar matasa ta kungiyar Bayer Leverkusen tun yana da shekara 10, wadda ta rarrashe shi ya shiga kungiyar.
A lokacin Havertz yana zaune a Aachen, don haka ya rika kai komo daga makaranta zuwa makarantar horas da 'yan wasa ta Leverkusen sau da dama a mako. Lokacin da ya shiga tawagar da ke buga wasan 'yan kasa da shekara 17, dan wasan ya tare a gidan mai bayar da sanarwa a filin wasa Klaus Schenkmann.
"Kai ya dace da fitowa daga iyalai masu saukin kai. Mahaifiyarsa da mahaifinsa suna da saukin kai," a cewar Jurgen Gelsdorf, tsohon shugaban makarantar horas da matasan 'yan kwallo ta Leverkusen.
Havertz ya rubuta jarrabawar kammala sakandare a yayin da yake tawagar manyan 'yan wasa ta Leverkusen, kuma ya taba cewa: "Ba zan iya tafiya makaranta ba da safe saboda muna atisaye."
A yayin da abokansa na makaranta suke tafiye-tafiyen bude ido zuwa Tafkin Lake Garda da ke kasar Italiya, shi kuwa Havertz ya soma shiga gasar Zakarun Turai inda suka fafata da Tottenham a filin wasa na Wembley a gaban 'yan kallo 85,000.
Ta yaya zai dace da murza leda a Chelsea?
Havertz zai iya taka leda a bangarori da dama.
Sai dai a matsayinsa na zabin farko, mai yiwuwa ya karbi lamba 10 a wasan da za a buga 4-2-3-1, ko kuma lamba takwas a wasan 4-3-3.
Sai dai tuni Chelsea ta samo 'yan wasan tsakiya, yayin da ta dauko Timo Werner, tana da zakakuran 'yan wasan biyu kenan da za su rika kai hari. Don haka ba sai ta gwada Havertz a wannan matsayi ba.
Yana iya kai komo tsakanin layuka ba tare da wata wahala ba sannan zai iya taka rawa ta musamman a tsakiyar Chelsea. 'Yan wasan kamarsu Christian Pulisic da Hakim Ziyech za su ji dadin murza leda tare da shi, yayin da 'yan wasan tsakiya za su neme shi idan suna tsaka mai wuya.