Adama Traore : Dan wasan ya kamu da cutar ne yayin yi wa Sifaniya aiki

Asalin hoton, Getty Images
Sifaniya za ta buga wasanta na gasar kasashen Turai ba tare da Adama Traore ba, bayan gwajin da aka yi masa aka ga yana dauke da Covid-19.
Kasar Sifaniya za ta buga wasannan farko da Jamus ne kafin daga bisani ta fafata da Ukrain.
Dan wasan gefe na Wolves ya kara zuwa wani gwaji ne a ranar Talata dan tabbatar da sakamakon da aka ba shi ya inganta.
Wannan sakamakon dai zai hana dan wasan shiga cikin tawagar kungiyar dan tabbatar da an bi dokar da hukumar kwallon kafa ta Turai Yefa ta tsara domin kare kai da 'yan kwallo baki daya.
Tuni aka cire sunan Mikel Oyarzabal saboda gaza tsallake gwajin da aka yi masa.
Duka 'yan wasan Luis Enrique sai da aka yi musu gwajin cutar da isarsu filin atisaye.
Sifaniya za ta fafata da Jamus a waje ranar Alhamis sannan ta karbi bakuncin Ukrain a gida ranar Lahadi wadanda duka suke a rukunin D.







