Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Coronavirus: David Silva ya kamu da cutar
Dan wasan Real Sociedad kuma tsohon dan kwallon Manchester City, David Silva ya kamu da cutar korona.
Dan wasan na ƙasar Sifaniya mai shekara 34 ya koma gasar La Liga ne a wannan watan bayan shafe tsawon shekara 10 yana taka leda a City.
Ya buga wa kungiyar wasa 436 ya kuma ci kofi 14.
Zuwa yanzu dan wasan bai nuna ko daya daga alamun cutar ba, sai dai tuni ya killace kansa.