Ward-Prowse zai sabunta zamansa a Southampton, Liverpool na son ɗauko Barnes daga Leicester

Dan wasan tsakiya na Southampton James Ward-Prowse, mai shekara 25, ya amince da sabuwar yarjejeniyar ci gaba da zama a kungiyar har shekarar 2025. (Telegraph - subscription required)

Liverpooltana son daukodan wasan Leicester City da Ingila mai buga tamaula a rukunin 'yan kasa da shekara 21 Harvey Barnes, mai shekara 22, idan aka soma musayar 'yan kwallo.(Mirror)

KazalikaLiverpool ta taya dan wasanSchalke da Turkiyya mai shekara 20, Ozan Kabak, wanda a baya Manchester City, Juventus da kuma Borussia Dortmund suka yi zawarcinsa. (Mail)

Borussia Dortmund ta soma tattaunawa da dan wasan Lille da Faransa Jonathan Ikone, mai shekara 22, a yayin da suke neman wanda zai maye gurbin dan wasan Ingila mai shekara 20 Jadon Sancho, wanda ake sa ran zai tafi Manchester United. (Times - subscription required)

KocinArsenal Mikel Arteta ya nuna alamar cewa zai shiga kasuwar musayar 'yan kwallon kafa saboda raunin da dan wasan Jamus Shkodran Mustafi, mai shekara 28, ya yi ya sanya an samu giɓi a tsaron bayan kungiyar. (Evening Standard)

Leeds United na fuskantar kalubale daga Lille a kokarinta na dauko dan wasan Gent da Canada Jonathan David, mai shekara 20, a cewar shugaban kungiyar ta Belgium Ivan de Witte. (De Zondag, via Express)

A gefe guda, Leeds ta so dauko dan wasanUruguay Edinson Cavini, mai shekara 33, bayan ya bar Paris St-Germain amma ya amince ya tafi Benfica. (Todo Fichajes)

KocinCeltic Neil Lennon yana son dauko dan wasan West Ham da Switzerland Albian Ajeti, mai shekara 23. (Daily Record)