An dakatar da Dier daga buga wasa hudu da cin tara

Eric Dier

Asalin hoton, Twitter: Insert Title

Bayanan hoto, Dier ya ce shiga 'yan kallon ba wata barazana ya kuma je ne don ya kare lafiyar dan uwansa

Hukumar kwallon kafar Ingila ta dakatar da dan wasan Tottenham, Eric Dier daga buga wasa hudu da cin tarar fam 40,000, bayan da ya shiga 'yan kallo zai kalubalanci wani mutun.

Lamarin ya faru a lokacin da Norwich City ta fitar da Tottenham daga gasar FA Cup.

Wannan hukuncin da FA ta yi wa dan kwallon mai shekara 26 na nufin ba zai buga wa Tottenham sauran wasannin da suka rage wa kungiyar a gasar Premier League ba.

An kuma ja kunnen dan kwallon da kada ya kara aikata irin halin nan gaba.

Wani kwamiti ne da aka kafa mai zaman kansa ya samu Dier da laifin, inda ya ce lamarin zai iya jefa dan kwallon cikin hatsari.

Ranar 4 ga watan Maris ne Norwich City ta fitar da Tottenham a karawar zagaye na biyar a FA Cup a bugun fenariti, inda Dier ya ci kwallo amma aka fitar da kungiyar.