Valencia ta sallami kocinta Albert Celades

Valencia ta kori kocinta Albert Celades wata tara da karbar aikin, yayin da daraktan wasannin kungiyar Cesar Sanchez ya ajiye mukamin.

An nada Voro Gonzalez domin maye gurbin Celades zuwa karshen kakar bana kuma karo na shida yana karbar aikin kocin rikon kwarya.

Ya fara karbar aikin kocin rikon kwarya a 2008 ya kuma hana kungiyar ta fada zuwa karamar gasar Spaniya, bayan da aka sallami Ronald Koeman.

An bai wa Celades aikin jan ragamar Valencia cikin watan Satumba, bayan da aka kori Marcelino.

Shi ne koci na shida da aka sallama daga aiki tun bayan da attajiri dan Singapore, Peter Lim ya sayi kungiyar a 2014.

Yayin da Sanchez wanda aka bai wa aikin daraktan wasannin kungiyar a Janairu - shi ne na shida da ya bar mukamin.

Valencia tana mataki na takwas a kan teburin La Liga ta kuma yi rashin nasara a wasa uku daga hudun da ta buga.