Gianluigi Buffon zai ci gaba da zama a Juventus kaka daya

Golan Juventus, Gianluigi Buffon ya tsawaita zamansa zuwa kaka daya a kungiyar da ke jan ragamar Serie A ta bana.

Tsohon mai tsaron ragar tawagar Italiya zai cika shekara 43 a lokacin da kwantiraginsa zai cika a Juventus a badi.

Ya sake komawa Juventus da tsaron raga a 2019, bayan kaka daya da ya yi a Paris St Germain.

Buffon ya buga wa Juventus wasannin Serie A sama da 500 tun lokacin da ya koma can a 2000.

Ya kuma fara sana'ar tamaula da kama gola a wasan farko a karawa da Parma a 1995.

Shima kyaftin din Juventus, Giorgio Chiellini ya sa hannu kan yarjejeniyar shekara daya.

Juventus wacce take ta daya a kan teburun bana ta bayar da tazarar maki hudu a gasar Serie A, kuma saura wasa 10 a karkare kakar shekarar nan.

Ita dai Juventus na fatan lashe kofin Serie A na bana kuma na tara a jere.