Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Juventus ta dauki Arthur Melo daga Barcelona
Barcelona ta sayar wa da Juventus dan wasa mai suna Arthur Melo.
Kungiyar ta Italiya za ta biya Yuro miliyan 72 da karin Yuro miliyan 10 na wasu tsarabe-tsarabe.
Dan wasan zai ci gaba da zama a Nou Camp har zuwa karshen kakar tamaula ta 2019/20.
Arthur ya koma Barcelona a 2018 daga Grêmio ya kuma buga wasa 72.
Ya fafata sau 47 a gasar La Liga da 10 a Copa del Rey da 13 a Champions League da wasa daya a Spanish Super Cup.
Dan wasan tawagar Brazil ya ci kwallo hudu a kaka biyu da ya yi a Barcelona.
Ya fara zura kwallo a ragar Osasuna a gasar La Liga ya kuma lashe kofin biyu da kuma Spanish Super Cup a kakar 2018/19.