Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Makomar Koulibaly, Pochettino, Skriniar, Hakimi, Moreno da Tagliafico
Liverpool na kokarin doke Manchester City kan dan wasan tsakiya na Napoli da Senegal Kalidou Koulibaly, mai shekara 29, inda za ta bayar da dan wasanta na baya Dejan Lovren na Croatia mai shekara 30, a yarjejeniyar. (Tuttosport via Sun)
Shugaban Inter Giuseppe Marotta ya ce kulub din ya yi nisa da tattaunawa kan dan wasan Borussia Dortmund Achraf Hakimi da Real Madrid ba ta aro. (Goal)
Chelsea ta samun kwarin guiwa bayan da kocin Ajax Erik ten Hag ya ce dan wasan baya na Argentina Nicolas Tagliafico da golan Kamaru Andre Onana, mai shekara 24, za su bar kulub din haka ma dan wasan Netherlands Donny van de Beek, da Manchester United ke nema ke hanyarsa ta barin kungiyar. (Express)
Manchester City na dab da sayen dan wasan gaba na Juventus da Sufaniya Pablo Moreno, mai shekara 18, inda za su yi musaya da dan wasan gaba da Portugal Felix Correia, mai shekara 19. (Goal)
Inter Milan ta fara tunanin sayar da dan wasan Slovakia Milan Skriniar, mai shekara 25, kuma Manchester City na cikin wadanda ke sha'awar dan wasan. Akwai yiyuwar za ta yi musaya da Sergio Aguero, mai shekara 32. (Calciomercato - in Italian)
Rahotanni sun ceBenfica na son dauko tsohon kocin Tottenham Hotspur Mauricio Pochettino a matsayin sabon kocinta. Kocin mai shekara 48 tun watan Nuwamba ba shi da kungiya. (Record - in Portuguese)
Dan wasan Ivory Coast kuma tsohon dan wasan Chelsea Salomon Kalou, mai shekara 34, wanda kwangilar shi ta kawo karshe a Hertha Berlin bayan kammala kaka yana dab da amincewa da sabuwar yarjejeniya zuwa kulub din kasar Brazil Botafogo. (Yahoo Sports)