Makomar Arthur, Pjanic, Pedro, Bellingham da Willian

Dan wasan tsakiya naBarcelonada Brazil Arthur, mai shekara 23, yana dab da amincewa da yarjejeniyar fam miliyan £72.5 zuwa Juventus, yayin da kuma dan wasan tsakiya na Bosnia Miralem Pjanic, 30, ke shirin amincewa da yarjejeniyar fam miliyan £54.25 zuwa Barcelona. (Sky Sports)

Dan wasan gaba da Sifaniya Pedro, mai shekara 32, zai koma Roma kan yarjejeniyar shekara biyu idan kwangilar shi da Chelsea ta kawo karshe bayan kammala kakar bana. (Sky Sports)

Bayern Munich ta janye wa Manchester United kan matashin dan wasan Birmingham mai shekara 16 Jude Bellingham, wanda kuma ya ja hankalin Borussia Dortmund. (Bild, via Sun)

Arsenal a shirye ta ke ta biya dan wasan Chelseada Brazil Willian, mai shekara 31, fam 250,000 duk mako kafin karshen annobar korona. (Mirror)

Leeds United na tattauna kan matashin dan wasan Ingila Jadan Raymond, mai shekara 16, bayan ya yi watsi da tayin Crystal Palace. (Athletic - subscription needed)

KocinTottenham Jose Mourinho ya shaida wa shugaban kulub din Daniel Levy cewa yana son cefanen sabbin 'yan wasa guda biyar. (90min)

Kocin Leicester Brendan Rodgers ya shaida wa James Maddison cewa Leicester ce ta fi dacewa da shi bayan alakanta dan wasan mai shekara 23 da Manchester United. (Leicester Mercury)

Dan wasan Real Madrid da Colombia James Rodriguez, mai shekara 28, wanda shekara daya ta rage masa har yanzu yana da damar komawa Napoli. (AS - in Spanish)

Arsenal da AC Milan suna hamayya kan dan wasan tsakiya na Red Bull Salzburg da Hungary Dominik Szoboszlai, yayin da Paris St-Germain ta fara fara yin magana kan dan wasan mai shekara 19. (Express)