Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
David Luiz zai ci gaba da zama a Arsenal shekara daya
Mai tsaron bayan Arsenal, David Luiz ya amince da yarjejeniyar shekara daya domin ya ci gaba da taka leda a kungiyar.
Haka ma mai tsaron baya, Pablo Mari da Cedric Soares za su zama mallakin Arsenal a karshen kakar bana.
Mari da Soares suna buga wa Gunners wasannin aro daga Flamengo da kuma Southampton da yarjejeniyar za ta kare da an kammala wasannin shekarar nan.
Shi kuwa Dani Ceballos wanda ke buga wasannin aro daga Real Madrid ya sa hannu kan kwantiragin tsawaita zamansa zuwa karshen kakar bana.
Luiz, dan wasan tawagar Brazil, mai shekara 33, ya koma Gunners daga Chelsea a bara, an kuma yi masa jan kati a wasan da Manchester City ta doke Arsenal 3-0 a gasar Premier da aka ci gaba.
Dan kasar Spaniya Marin, mai shekara 26 da na Portugal, Soares, mai shekara 28 za su sa hannu kan kunshin yarjejeniyar da Arsenal za ta gabatar musu a watan gobe.