Bayern za ta lashe Bundesliga na takwas a jere ran Talata

Werder Bremen za ta karbi bakuncin Bayern Munich a wasan mako na 32 a gasar cin kofin Bundesliga ranar Talata.

Da zarar Bayern ta ci Werder za a damka mata kofin gasar bana kuma na takwas a jere na 30 jumulla.

Bayern ta jera lashe kofin Bundesliga bakwai tun daga 2012/13, bayan da ta karba a hannun Borrusia Dortmund.

A wasan farko a kakar bana da suka fafata ranar Asabar 14 ga Disambar 2019, Bayern ce ta yi nasara da ci 6-1.

Wadanda suka ci wa Bayern kwallayen sun hada da Thomas Mueller da Robert Lewandowski da ya ci biyu da Philip Coutinho da ya ci uku rigis.

Bayern tana mataki na daya a kan teburi da maki 73 ta kuma ci wasa 23 da canjaras hudu aka kuma doke ta a wasa hudu.

Haka kuma ta ci kwallo 92 aka zura mata 31 tana da rarar 61 kenan, bayan wasa 31 da ta yi a kakar 2019-20.

Robert Lewandowski na Bayern Munich shi ne ke kan gaba a cin kwallaye a kakar shekara nan da 30 a raga

  • Robert Lewandowski Bayern Munich 30
  • Timo Werner RB Leipzig 25
  • Jadon Sancho Borussia Dortmund 17
  • Rouwen Hennings Fortuna Dusseldorf 14
  • Wout Weghorst Wolfsburg 14
  • Jhon Cordoba FC Koln 13
  • Sebastian Andersson FC Union Berlin 12
  • Florian Niederlechner FC Augsburg 12
  • Robin Quaison FSV Mainz 05 12
  • Serge Gnabry Bayern Munich 12
  • Kai Havertz Bayer 04 Leverkusen 11
  • Erling Haaland Borussia Dortmund 11
  • Marco Reus Borussia Dortmund 11

Wasannin makon na 33 da za a buga a karkare kakar bana

Ranar Asabar 20 ga watan Yuni

  • Bayern Munich da SC Freiburg
  • Schalke 04 da Wolfsburg
  • FC Koln da Eintracht Frankfurt
  • FSV Mainz 05 da SV Werder Bremen
  • Hoffenheim da FC Union Berlin
  • Fortuna Dusseldorf da FC Augsburg
  • S C Paderborn 07 da Borussia Monchengladbach
  • RB Leipzig da BV Borussia Dortmund