Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mahukuntan La Liga za su hukunta wanda ya shiga fili zai yi hoto da Messi
Mahukuntan La Liga sun ce za su dauki mataki na shari'a kan wanda ya shiga fili zai dauki hoto tare da Messi a ranar Asabar.
Barcelona ta ci gaba da zama ta daya a kan teburin La Liga, bayan da ta doke Real Mallorca 4-0, kuma Messi ne ya ci na karshe na 20 jumulla a bana.
Mutumin mai sanye da rigar Argentina mai dauke da sunan Messi ya shiga cikin fili a lokacin da ake tsaka da wasa a zagaye na biyu a karawar da aka yi ba 'yan kallo.
Ya kuma samu damar yin hoton, amma dan nesa da Messi kafin jami'an tsaro su damke shi.
Mahukunta La Liga sun ce sun dauki lamarin da girma, domin za a iya jefa lafiyar mutane cikin hadari da kuma kaskantar da gasar ta Spaniya a idon duniya.
Mutumin ya ce ya haura katanga ne mai tsawon mita biya ya samu shiga filin wasa na Mallorca.
Ya kuma kara da cewar ya dade ya na wannan shirin, kuma tun lokacin da ya ji za a buga wasan ya tsara yadda zai je ya yi hoto da kyaftin din Argentina nan.