To Jama'a nan na kawo karshen gabatar muku da shirin na labarin wasanni kai tsaye da fatan za ku tara a shirimnmu na gaba.
Sunana Mohammed Abdu Mamman Skeeper TW ke muku fatan alheri mu sake haduwa a shirin gaba.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da zai ke zuwar muku da labarin wasanni kai tsaye kan gasar Bundesliga karawar mako na 31 da sauran labarin wasanni da ke gudana a sassan duniya.
Mohammed Abdu
To Jama'a nan na kawo karshen gabatar muku da shirin na labarin wasanni kai tsaye da fatan za ku tara a shirimnmu na gaba.
Sunana Mohammed Abdu Mamman Skeeper TW ke muku fatan alheri mu sake haduwa a shirin gaba.
Barcelona ta ci gaba da zama ta daya a kan teburin La Liga bayan da ta samu maki uku a kan Real Mallorca.
Koda Real ta ci Eibar ranar Lahadi, Barcelona za ta ci gaba da zama ta daya da tazarar maki biyu amma yanzu dai tazarar maki biyar kenan kan Real ta buga wasanta.
Kuma na 200 da Zinedine Zidane zai ja ragamar Real Madrid a matsayin koci.
Lionel Messi ya ci kwallo na 20 a gasar La Liga kuma karo na 12 a jere.
A manyan gasar kwallon kafar nahiyar Turai babu wanda ya yi wannan bajintar tun daga kakar tamaula ta (2008-09-2019-20).
Cristiano Ronaldo ya yi wannan bajintar da kaka 11 da ya dunga cin kwallo 18 a gasar Premier League tare da Man United itun daga 2008-09.
Jordi Alba ya ci kwallo na uku mai kyau kuma ya yi murnar cin kallon mai kayatarwa.
Luis Suarez na saka kaimi ko zai ci kwallo na hudu imnda ya samu damai zai fita a guje sai mataimakin alakalin wasa ya daga tuta cewar ya yi satar gida.
Tun farko sai da aka yi tantamar kwallon da Jordi Alba ya ci yana ganin kamar ya yi satar gida daga bangaren hagun fili sai da aka je aka duba VAR ta tabbatar da satar gida.
Da alama Barcelona ta hada maki uku a wasan nan za ta ci gaba da zama ta biyu ko da Real ta doke Eibar a ranar Lahadi
Napoli ta kai wasan karshe a Copa Italiya za ta fafata da Juventus ranar Laraba.
Wasa na 300 da dan kwallon ke yi a Barcelona.
'Yan kwallon Barcelona, Arthur da Nelson Semedo za su shiga filin saura minti 20 a tashi wasa.
Kwallo mai kyau da aka yi ta bani in baka tsakanin Suarez da ya bai Messi tun farko shi ya sawa Suarez kwallo ya kuma mayar masa da ita sai Messi ya nemi raga amma kwallon ta bude ta yi waje.
Luis Suarez ya dawo wasa kenan. Y canji Antoine Griezmann.
An sa ran Suarez ba zai sake buga kwallo ba a kakar bana kan raunin da ya yi.
Sai dai cutar korona ta tsayar da komai tun cikin watan Maris hakan ya ba shi damar murmurewa har zai ci gaba da buga gasar bana.
Ivan Rakitic ya shiga fili dan kwallon Barcelona inda ya maye gurbin Arturo Vidal wanda ya ci kwallon farko..
Mallorca ta saka 'yan wasa biyu.
Mallorca ta kusan zare kwallo daya bayan da Dani Rodriguez ya bai wa Ante Budimir shi kuma ya buga kwallo ta je wajen gola.